Tsananin zafin rana da ya kai ma’aunin CELSIUS 49 ya yi sanadiyyar mutuwar alhazai da galabaitar wasu musamman yayin tafiya jifar Shaidan a Makkah.
Mutane bakwai ne suka mutu yayin da wani jirgin kasan fasinja da na dakon kaya suka ci karo da juna a ranar Litinin a jihar Bengal ta Yamma a Indiya, lamarin da ya lalata karusan fasinja guda uku, in ji 'yan sanda.
Firai Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya rusa majalisar zartaswar yakin Isra'ila da aka dorawa alhakin jagorantar yakin Gaza, a cewar jami'an Isra'ila a ranar Litinin.
A jiya Lahadi Isra'ila ta fadi cewa, zata fara tsagaita wuta a hare haren da take kai kan mayakan Hamas a kudancin Gaza tsawon sa’o’i 11 a duk rana, don bada damar kai karin kayan agaji ga Falasdinawan da ke fama da yunwa.
A yau Juma'a ne babbar kotun kasar Nijar ta dage rigar kariyar hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, lamarin da zai bada damar a yi masa shari'a bayan hambarar da shi a watan Yulin 2023.
Ta yiwu ranar Alhamis kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a kan wani kuduri da Birtaniyya ta gabatar da daftarinsa.
Shugaban Amurka Joe Biden da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy za su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ranar Alhamis, yayin da za su gana a Italiya a gefen taron kolin kungiyar kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya.
An kama wasu mutane takwas daga kasar Tajikistan da ake zargin suna da alaka da kungiyar IS a Amurka a cikin 'yan kwanakin nan, a cewar wasu da ke da masaniya kan lamarin.
Sama da mutane 35 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata gobara ta tashi a wani gini da ke dauke da kusan ma'aikata 'yan kasashen waje 200 a Kuwait, kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Laraba.
Wani kwale-kwale da ke dauke da bakin haure ya nutse a yankin tekun Yemen, inda mutane akalla 49 suka mutu, yayin da wasu 140 suka bace, a cewar hukumar kula da baki 'yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya da ake kira IOM a ranar Talata.
Wasu jami’an Amurka biyu sun ce shugaba Joe Biden ne ya amince da matakin tura makaman.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Sin, a yau Talata, ya ce, an kai wadanda suka jikkata asibiti, kuma babu wanda ke cikin mawuyacin hali.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.