Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netanyahu Ya Rusa Majalisar Ministocin Yakin Isra'ila


Isra’ila
Isra’ila

Firai Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya rusa majalisar zartaswar yakin Isra'ila da aka dorawa alhakin jagorantar yakin Gaza, a cewar jami'an Isra'ila a ranar Litinin.

Netanyahu ya dauki wannan matakin ne jim kadan bayan da wani babban jami'in hukumar ya yi murabus daga gwamnatin kasar saboda takaicin yadda Isra'ila ke kai wa Gaza hare-hare.

An kyautata zaton haka ba zai rasa nasaba ba da ficewar Benny Gantz, tsohon hafsan soji, daga gwamnatinsa a farkon wannan watan da muke ciki.

Rashin Gantz a gwamnatin ya tursasa Netanyahu yin dogaro da abokan adawarsa wajen gudanr da ayyukan gwamnati wanda rusa majalisar ministocin yakin ya tabattar da canjin, yayin da yakin da aka kwashe watanni takwas ana yi a Gaza ya ci gaba.

Jami’an wadanda suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da damar tattaunawa da manema labarai kan sauyin, sun ce nan gaba dai Netanyahu zai zanta da wasu daga cikin mambobin gwamnatinsa kan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi yakin.

Hakan ya hada da majalisar ministocinsa na tsaro, inda abokan hamayyar gwamnati masu adawa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma nuna goyon bayansu ga sake mamaye Gaza, su ne mambobi.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG