Guguwar da aka yi mata lakabin Alberto ta yi kaca-kaca da arewa maso gabashin Mexico da sanyin safiyar Alhamis a matsayin guguwar farko da aka ambata a kakar bana, dauke da ruwan sama mai karfi da ya yi sanadin mutuwar mutane uku, amma ya kawo jimami mai kyau ga yankin mai fama da matsanancin fari
Akalla mutane biyu ne suka mutu yayin da wasu tara suka jikkata yau Alhamis a lokacin da wani jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi ci karo da wani jirgin kasa mai gwajin aiki a babban birnin kasar Chile, Santiago.
Ministan kula da Ma'adanai na Nijar ya bai wa kamfanin ORANO da ke aikin hakar ma'adanin Uranium a kasar wa'adin kwanaki uku ko ya fara aiki ko kuma a soke lasisinsa
A ranar Larabar nan ne Indiya ta yi fama da matsanancin yanayi da ya haifar da tsananin zafi da zabtarewar kasa da kuma ambaliyar ruwa.
Wani babban jirgin ruwan dakon kaya ya nutse 'yan kwanaki bayan wani harin da 'yan tawayen Houthi na Yaman suka kai masa, kuma ana kyautata zaton harin ya kashe wani mutum a cikin jirgin, a cewar hukumomi da safiyar Laraba, wanda shi ne jirgi na biyu da ya nutse sanadiyyar hare haren 'yan tawayen.
Shugabannin kasashen Koriya ta Arewa da na Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a ranar Larabar nan, wadda ta kara zurfafa hadin gwiwarsu ta soji, da ta hada da alkawarin kare juna, na taimakon juna idan har aka kai wa daya hari, inda Kim Jong Un na Arewa ya kira sabuwar alakar da "kawance".
Daruruwan mahajjata ne suka mutu bana a yayin gudanar da aikin hajjin shekara-shekara da Musulmi ke gudanarwa a Makka sanadiyar tsananin zafi, kamar yadda rahotannin manema labarai da ma'aikatun harkokin waje suka bayyana.
Wakilan Sudan sun zargi Hadaddiyar daular larabawa da taimaka wa dakarun RSF ta hannun mayakan sa-kai dake Chadi, kudancin Libya da kuma birnin Khartoum.
Shugaba Joe Biden ya sanar da wani sabon tsari da zai ba wadanda su ka auri Amurkawa, da kuma 'ya'yan mutanen da su ka auri Amurkawa, izinin zama kasar din-din-din.
Hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama a ranar Talata sun hallaka akalla Falasdinawa a wasu sansanonin zirin gaza 2 masu tarihi, a yayin da tankokin Isra'ila ke kara kutsawa zuwa kudancin birnin Rafah, a cewar mazauna yankin da ma'aikatan lafiya.
A jiya Talata babban jami'in kare hakkin 'bil adama na MDD yayi gargadin halin tauyen hakkin da ake fuskanta a gabar yamman kogin Jordan ciki harda yankin gabashin birnin Kudus na kara tabarbarewa yayin da ake cigaba da fuskantar mace-mace da wahalhalun babu gaira babu dalili a zirin Gaza
Shugaban fadar Kremlin ta Rasha, Vladimir Putin ya taya takwaransa na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa murnar sake lashe zabensa a matsayin shugaban kasa a Litinin din data gabata.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.