Okonjo-Iweala tayi wannan kira ne yayin wata tattaunawa a kan haraji a taron kolin tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Davos, na kasar Switzerland, a makon da aka jiyo shugaban Amurka Donald Trump yana barazanar kakaba haraji akan China da tarayyar Turai da kasashen Mexico da Kanada.
"Son Allah kada mu rura wannan wuta. Na san cewar mun taru anan ne domin tattaunawa akan harajin kasuwanci, na sha yin kira ga kowa akan mu bi al'amura a hankali, haka kuma yanzu na fahimci cewar ana matukar rura wutar," a cewarta.
Ta yi waiwaye akan abin da da dokar harajin Smoot-Hawley ta haifar a Amurka lokacin durkushewar tattalin arziki ta 1930, abin da ya sabbaba daukar fansa da kara tabarbara rikicin tattalin arzikin wancan lokaci.
"Muna shaidawa mambobinmu a wto cewar, akwai wasu hanyoyin da za'a iya bi. koda an kakaba maka haraji, don Allah kada ka tada hankali, kada ka wayi gari ba tare da bin tsare-tsaren da suka dace ba kaima ka kakaba naka," a cewarta.
Dandalin Mu Tattauna