Da ya ke tabbatar da ranar 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zabe, Steinmeier ya jaddada bukatar samun “kwanciyar hankalin siyasa” sannan ya bukaci a gudanar da yakin neman cikin mutunci da kyautatawa”.
Babban darektan Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce shi da tawagar sa suna babban filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa dake Sana’a babban birnin kasar Yemen lokacin da Isra’ila ta kai hari.
Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ya ayyana yau Alhamis ta zamo ranar makoki tare da soke shirin tafiyarsa zuwa Rasha domin halartar taron kolin kasashen da suka balle daga tsohuwar tarayyar Soviet (CIS).
Tashar ta bayyana sunayen ma'aikatan nata Da Faisal Abu-Qumsan da Ayman Al-Jadi da Ibrahim Al-Sheikh Khalil da Fadi Hassouna da kuma Muhammad Al-Lada'a.
Wannan shine mummunan hari na 13 kan turakun lantarkin Ukraine, kuma shi ne samamen Rasha na baya-bayan nan kan tsarin lantarkin kasar a wannan hunturun.
Wani jirgin saman fasinja kirar Embraer da ya taso daga Azerbaijan zuwa Rasha ya rikito a kusa da birnin Aktau na kasar Kazakhstan a yau Laraba dauke da fasinjoji 62 da ma'aikata 5, kamar yadda hukumomin Kazakhstan suka sanar, inda suka ce mutane 27 sun tsallake rijiya da baya.
A gaban dubban mabiya darikar da suka yi dafifi a kofar majami'ar St. Peter’s Basilica dake birnin Rome, Paparoman ya kuma bukaci samun tsagaita wuta a Gaza da sakin Yahudawan da kungiyar Hamas ke garkuwa dasu a can.
A yau Laraba Kiristoci a fadin duniya ke gudanar da bikin Kirsimeti domin murnar zagayowar ranar haihuwar Isa Almasihu.
Lissafi ne mai sauki amma maras dadi. Yawan mutanen dake fama da yunwa ko ke fadi tashin rayuwa na kara karuwa a fadin duniya, a yayin da yawan kudaden da kasashe masu arziki ke bayarwa a matsayin gudunmowa da nufin tallafa musu ke raguwa.
Hauhawar farashin kayan masarufi ya ragu a galibin kasashen duniya a 2024, sai dai hakan bai damu masu kada kuri’a ba
Domin Kari
No media source currently available