Sanarwar da ma'aikatar agajin gaggawa ta kasar dake tsakiyar nahiyar Asiya ta fitar tace, ma'aikatan kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar kuma wadanda suka tsira da rayukansu ciki har da yara 3 na samun kulawa a wani asibitin dake kusa da wurin.
Kamfanin jiragen saman kasar Azerbaijan ya ce an tilastawa jirgin, wanda ya jima yana jigila tsakanin baku zuwa Grozny, babban birnin yankin Chechnya na Rasha, yin saukar gaggawa a wani wuri dake da tazarar kilomita 3 daga birnin Aktau na Kazakhstan.
Kamfanonin yada labaran kasar Rasha sun ce an sauyawa jirgin akala ne saboda yanayin hazo da aka tashi da shi a birnin Grozny.
Dandalin Mu Tattauna