Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Isra'ila A Gaza Ya Hallaka 'Yan Jarida 5


Tashar ta bayyana sunayen ma'aikatan nata Da Faisal Abu-Qumsan da Ayman Al-Jadi da Ibrahim Al-Sheikh Khalil da Fadi Hassouna da kuma Muhammad Al-Lada'a.

Wata tashar talabijin din Falasdinu da ke da alaka da wata kungiyar mayaka tace harin Isra'ila ya kashe mata 'yan jarida 5 a cikin motar da suke ciki a Gaza a yau Alhamis , yayin da rundunar sojin Isra'ilar ta yi ikirarin cewa ta kai harin ne kan wani "kurkukun 'yan ta'adda".

Wani makami mai linzami ne ya afka kan motar aikin da 'yan jaridar ke ciki sa'ilin da take ajiye a sansanin 'yan gudun hijira na al-Nuseirat dake tsakiyar Zirin Gaza, a cewar sanarwar da kafar da suke yiwa aiki, "Al-Quds Today", ta fitar

Tashar talabijin din na da alaka da kungiyar Islamic jihad wacce mayakanta ke yaki tare da Hamas a zirin Gaza kuma sun taka rawa a harin da aka kaiwa Isra'ila na ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da ya sabbaba barkewar yaki a yankin na Falasdinu.

Tashar ta bayyana sunayen ma'aikatan nata Da Faisal Abu-Qumsan da Ayman Al-Jadi da Ibrahim Al-Sheikh Khalil da Fadi Hassouna da kuma Muhammad Al-Lada'a.

An hallaka su yayin da suke gudanar da ayyukansu na yada labarai da bada agaji", a cewar sanarwar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG