Dokar ta soji ba ta bayyana wani dalili na korar Tambela ba, wanda aka nada matsayin firimiyan rikon kwarya jim kadan bayan Traore ya kwace mulki a watan Satumban shekara ta 2022.
Taron zai gudana ne a gefen babban taron Doha, wani taron shekara-shekara da ke tattara hancin manyan jami'ai, malamai da shugabannin 'yan kasuwa daga kasashe fiye da 150, domin tattauna batutuwan da suka shafi juna.
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na X, Zelenskyy ya ce makamin na jirgin sama maras matuki mai suna "Peklo" - wanda ke nufin "wuta" a harshen kasar Ukraine - yana cin nisan zangon kilomita 700, da karfin gudun kilomita 700 a cikin sa'a guda.
Kotun daukaka kara a Washington ta amince da hujjojin da gwamnatin tarayya ta gabatar cewa TikTok na da hatsari ga tsaron kasa, saboda yana tattara bayanai masu yawa game da masu amfani da shi, da kuma saboda a ƙarshe gwamnatin China tana da karfin iko kan uwar kamfanin, ByteDance.
Rundunar sojin Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 39 a wasu munanan hare-haren da ta kaddamar a fadin zirin Gaza cikin daren jiya Laraba
A yau Laraba tankokin yakin Isra’ila suka matsa zuwa yankunan arewacin Khan Younis dake kudancin zirin Gaza kuma jami’an bada agajin Falasdinu sun ce hare-haren Isra’ilar ta sama sun hallaka akalla mutane 20 a fadin zirin
Wani babban jami’in gwamnatin Ukraine ya kai ziyara Amurka domin kulla alaka da gwamnatin zababben shugaban kasa Donald Trump, wanda ya sha alwashin kawo karshen yakin Rasha a Ukraine da ya kama aiki, kamar yadda kafar yada labaran Ukraine ta ruwaito Ministan Harkokin Wajen kasar ya fada yau Laraba
Majalisar Dinkin Duniya ta nemi agajin dala biliyan 47 a shekarar 2025 domin taimakawa mutane kusan miliyan 190 da ke gujewa rikici da yunwa.
A cewar fadar White House, ziyarar Biden ta kasance irinta ta farko da wani shugaban Amurka mai ci ya taba kaiwa kasar Angola, kuma ita ce ziyarar farko da wani shugaban Amurka ya kai yankin kudu da saharar Afirka tun cikin shekarar 2015.
Harin ya sabbaba daukewar lantarki a wani sashe na birnin Ternopil, a cewar magajin garin yankin, mako guda bayan da hare-haren Moscow suka katse lantarki ga galibin birnin da kewayensa.
Sabunta hare-haren roka da mayakan Hezbullah suke yi a Lebanon, da kuma hare-haren ramuwar gayya da Isra'ila ke kai wa, su na kara matsin lamba kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta ‘yan kwanaki da aka cimma, da nufin kwantar da tarzoma a yankin da ke fama da rikici.
Domin Kari
No media source currently available