Sun yi wannan tattaunawa yau talata a gefen taron kolin kasashe masu arzikin man gas na uku da ake gudanarwa a Teheran, babban birnin Iran.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yana halartar taron kolin kasashe masu arzikin man gas da aka bude yau litinin a Teheran, babban birnin kasar Iran
Ranar 19 ga watan Nuwamba Hukumar Da Ke Kula Da Ma'aikatun Yada Labarun Amurka Ta BBG, wadda VOA ke karkashin ta, ta karrama ma'aikata ciki har da na Sashen Hausa na Muryar Amurka. Nuwamba 19, 2015.
Wannan ya biyo bayan mamaye hotel din Radisson Blu da wasu 'yan bindiga suka yi su na garkuwa da mutane wajen 170, tare da kashe 3 daga cikin wadanda suke yin garkuwa da su din.
Hotunan wadanda suka ji rauni suke kwance a asibiti da kuma wuraren da bam ya tashi a kasuwar wayar hannu dake Farm Centre a Kano
Hotuna daga kowace kusurwa ta duniya a yau talata 17 ga watan Nuwamba 2015.
Yayin da aka sako Mohammed Abdesalam, har yanzu ana farautar dan'uwansa Salah, yayin da wani dan'uwan nasa mai suna Ibrahim yana cikin wadanda suka mutu a lokacin harin na Paris, Nuwamba 16, 2015.
Jama'a da dama a wurare daban daban sun yi addu'oi da nuna alhinin su dangane da mummunan harin da aka kai a birnin Paris, Nuwamba 15, 2015.
A bayan hare-haren da suka kashe mutane akalla 127, wadanda kungiyar ISI ta ce ita ce ta kai, Faransawa su na ci gaba da jimami yayin da shugabanninsu ke lasar takobin cewa wadanda suka kai zasu ga tashin hankali.
Domin Kari