A bayan hare-haren da suka kashe mutane akalla 127, wadanda kungiyar ISI ta ce ita ce ta kai, Faransawa su na ci gaba da jimami yayin da shugabanninsu ke lasar takobin cewa wadanda suka kai zasu ga tashin hankali.
Faransawa Na Ci Gaba Da Jimamin Wadanda Suka Mutu Ko Suka Ji rauni
A bayan hare-haren da suka kashe mutane akalla 127, wadanda kungiyar ISI ta ce ita ce ta kai, Faransawa su na ci gaba da jimami yayin da shugabanninsu ke lasar takobin cewa wadanda suka kai zasu ga tashin hankali.

1
Ma'aiukatan agaji su na duba mutanen da aka kashe ko aka ji musu rauni a kofar wani gidan abinci a Paris.

2
'Yan sanda su na yin sintiri a gundumar nan ta Place de la Republique dake birnin Paris asabar, kwana guda a bayan wasu munanan hare-haren da suka kashe mutane fiye da 100.

3
Sojojin Faransa su na yin sintiri a kusa da hasumiyar nan ta Eiffel Tower, kwana guda a bayan munanan hare-hare a birnin Paris.

4
Wasu daga cikin wadanda suka kubuta da rayukansu a dakin wasa na Bataclan dake Paris a daren Jumma'a 13 Nuwamba, 2015.