Yajin aikin na zuwa ne bayan cikar wa’adin makonni 3 da likitocin suka bayar a shekarar da ta gabata.
An samu Beatrice da mijinta Sanata Ike Ekweremdu da laifin yunkurin safara da cinikin sassan jiki bil adama a London a watan Mayun 2023
A cewar sanarwar da CBN din ya fitar, kunshin dokokkin zai zamo jagora ga bangaren bankuna wajen dabbaka halaye nagari a tsakanin dillalan da aka sahalewa yin hada-hada a kasuwar musayar kudaden Najeriya.
Matakin ya dace da aniyar gwamnatin ta tallafawa kamfanonin jiragen saman Najeriya tare da bunkasa bangaren sufurin jiragen saman.
Mutum kusan 100 ne suka rasa rayukansu a hatsarin tankar man da ya auku a Suleja a lokacin da suke kokarin kwasar man fetur a ranar Asabar.
An kama Seyni Amadou, babban editan gidan talabijin na Canal 4, in ji kungiyar CAP-Medias-Niger, mai wakiltar ma'aikatan yada labarai a kasar. A ranar Juma'ar da ta gabata ma'aikatar sadarwa ta Nijar ta sanar da dakatar da tashar ta shi na tsawon wata guda.
Akalla mutane 60 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a arewacin Najeriya a yau Asabar bayan da wata motar dakon mai ta kife, ta kuma zubar da mai da kafin daga bisani ta fashe, a cewar hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC).
Majalisar dokokin Najeriya ta yi watsi da kasafin kudin Ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ta kasa da dukkan hukumomin da ke karkashin ma'aikatar.
Wannan satar za ta haddasa rashin wuta a unguwannin Maitama, Wuse, Jabi, Life Camp, Asokoro, Utako da Mabushi.
Rahoton ya kara da cewa sauye-sauyen baya-bayan nan da gwamnatin Najeriyar ke aiwatarwa sun taimaka wajen bunkasa kwarin gwiwar yin kasuwanci.
Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta jaddada cewa har yanzu Julius Abure ne shugaban jam’iyyar Labour na kasa.
Domin Kari
No media source currently available