Ibtila'i ya afkawa karamar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, sakamakon tashin gobara a wata makarantar tsangaya wacce ta hallaka akalla almajirai 17.
Tuni aka birne almajiran 17 a yau Laraba a bisa tsarin addinin Musulunci.
Gobarar wacce ta fara tashi da misalin karfe 1:45 na safiyar yau Larabar, kuma tayi ta ci tsawon sa'o'i 3, inda ta hallaka almajirai 17 tare da jikkata wasu 16, ta samo asali ne sakamakon tashin wuta daga kara, inda ta kone wurin da almajirai ke kwana.
Malam Aliyu Abubakar Khalifa, malamin almajiran, wadanda suke yan tsakanin shekaru 10 zuwa 16, ya ba da bayanin abin da ya faru yana zubar da hawaye,.
Ya ce, "gobarar ta tashi ne da tsakar dare kuma an fara kashe ta,".
"Mun ce yaran kowa ya koma wajen baccin shi, amma an dan kara jimawa kadan sai muka ji ana ta kururuwa cewa wuta wuta a kawo agaji, ana ta kururuwar 'wuta, wuta!' Na garzaya waje da gudu na tarar da almajirai kusan 30 a kasa, suna ta kokarin tserewa," in ji shi.
To sai dai hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara ta kasa kai masu dauki cikin gaggawa sakamakon lalacewar motar kashe gobara a cewar Khalifa.
Ya kara da cewa jami'an 'yan sanda da sauran al'umma sun taimaka wajen kashe wutar da kuma ceto wasu daga cikin daliban.
Khalifa ya tabbatar da cewa daga cikin almajirai kusan 100 da ke cikin gidan, 17 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 16 suka samu raunuka inda yace "asara ce mai muni, amma mun mayar da komai ga Ubagiji."
Sai dai shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara mai kula da yankin Kaura Namoda, Abdulmudallib Muhammad Galadi yace “da karfe 2:25 na safe ne aka kawo mana rahoton faruwar lamarin" kuma ba su samu damar kai daukin gaggawa ba saboda "matsalar lalacewar motar su ta kashe gobarar".
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara wadda ta tabbatar da faruwar Lamarin ta bakin jami’in hulda da jama’a na Rundunar DSP Yazid Abubakar yace mutane 17 ne suka mutu yayin da wasu 17 suke kwance a asibiti suna samun kulawar likitoci.
“Lokacin da abun ke faruwa jami’an mu sun hanzarta zuwa wurin, sun kwashi marasa Lafiya zuwa asibiti kuma suka taimaka wajen ganin bada kulawa har Allah yasa aka kashe wutar.” Inji DSP Yazid.
Wannan lamari dai ya jefa al’umma cikin rudani yayin da suke alhinin da jimamin rasuwar kananan yaran sanadiyyar gobara.
Saurari rahoton Abdulrazak Kaura Bello:
Dandalin Mu Tattauna