Jami’an gwamnatin Najeriya sun kafa wani kwamitin da zai samar da wani tsari mai dorewa wanda zai maye gurbin Shirin tallafin lafiyar da asususun raya kasashe masu tasuwa USAID yake daukan nauyinsu biyo bayan matakin Trump na dakatar da shirye shiryen asusun tallafin na tsawon kwanaki 90. Manufar kwamitin da ya kunshi ministoci daban daban ita ce tabbatar da ya samo tallafin kudin da za su tallafa wa shirye shiryen lafiya masu mahimmaci.
Wakilin Muryar Amurka a Abuja, Timpothy Obiezu, ya ba da rahoton cewa, ministan lafiyar Najeriya y ace kwamitin ya kunshi jami’ai daga ma’aikatar kudi, lafiya da muhalli, domin tabbatar da cewa masu shan maganin HIV, tarin fuka da malariya ba su fuskanci wata komabaya ba yayin da ake fuskantar rashin tabbas akan dokokin Amurka.
Bada jimawa ba bayan da ya karbi ragamar mulki makonni 2 da suka gabata, Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umurnin dakatar da ayyukan tallafin Amurka tsawon kwanaki 90. Sai dai ‘yan kwanaki bayan nan, ya amince da ci gaba da bada tallafin wucin gadi don ceton rai a bangaren agajin jinkai, da suka hada da magunguna, kulawar lafiya, abinci da muhalli.
Duk da wannan matakin, har yanzu akwai fargaba akan abin da zai kasance nan gaba a bangaren tallafin da Amurka ke bayarwa a fannin lafiya a fadin duniya.
Najeriya tana doga cikin kasashen da suke samun tallafi mai tsoka daga tallafin da Amurka ta ke bai wa kasashen waje, inda a 2023 ta samu tallafin dalar Amurka biliyan $1.02, galibi daga hukumomi irin su USAID.
Dandalin Mu Tattauna