Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Kara Kasafin Kudin 2025 Zuwa Naira Tiriliyan 54.2


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Karin kasafin kudin ya samo asali ne sakamakon samun karin kudin shiga na Naira tiriliyan 1. 4 daga hukumar tara kudaden shiga ta Najeriya (FIRS), da Naira tiriliyan 1.2 daga hukumar yaki da fasakwabrin kasar (NCS) da kuma Naira tiriliyan 1.8 da sauran hukumomin gwamnati suka tara.

Shugaba Bola Tinubu ya kara yawan kasafin kudin 2025 daya gabatar daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa 54.2, inda ya kafa hujja da samun karin kudaden shiga daga wasu muhimman hukumomin gwamnati..

Shugaban kasar ya isar da sakon yiwa kasafin kudin kwaskwarima ne a cikin mabambantan wasikun da ya tura wa Majalisar Dattawa da ta Wakilai, wadanda shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya karanta a zaman majalisar na yau.

A cewar Shugaba Tinubu, karin kasafin kudin ya samo asali ne sakamakon samun karin kudin shiga na Naira tiriliyan 1. 4 daga hukumar tara kudaden shiga ta Najeriya (FIRS), da Naira tiriliyan 1.2 daga hukumar yaki da fasakwabrin kasar (NCS) da kuma Naira tiriliyan 1.8 da sauran hukumomin gwamnati suka tara.

Biyo bayan sanarwar, shugaban Majalisar Dattawan ya mika bukatar shugaban kasar ga kwamitin majalisar a kan kasafi domin yin nazarin gaggawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG