Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Samu $831.14bn Daga Cinikin Mai Da Iskar Gas A Shekaru 24 - NEITI


Satar danyen man da ake yi tsawon shekaru ta janyowa kasar asarar da aka kiyasta cewar ta kai ganga miliyan 701.48 tun a shekarar 2009, lokacin da NEITI ta fara bin diddigin asarar da aka yi.

Hukumar tabbatar da gaskiya da adalci a hakar ma’adinai a Najeriya (NEITI) ta bayyana cewar Najeriya samu kudin shigar da ya zarta dala biliyan 831.14 daga bangaren man fetur da iskar gas tsakanin 1999 da 2023.

Babban sakataren NEITI, Ogbonnaya Orji, ne ya bayyana hakan a jiya Litinin sa’ilin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan asusun ajiyar gwamnati.

Ya kara da cewa kasar na bukatar dala biliyan 20 a duk shekara, nan da shekaru 10 masu zuwa ,domin bunkasa gine-gien da sauran kayayyakin aikin da ta ke da su a bangaren iskar gas.

Kwamitin, karkashin jagoranci Sanata Ahmad Wadada, na karbar bayanai ne kan sakamakon binciken NEITI mai sassa 16 da ya karade kamfanoni 78 da ke bangaren hakar ma’adinai.

Shugaban hukumar ta NEITI ya kuma ayyana cewa Najeriya ta samar da fiye da dala biliyan 831.14 na kudin shiga daga bangaren man fetur da iskar gas tsakanin 1999 da 2023.

Sai dai ya kara da cewa satar danyen man da ake yi tsawon shekaru ta janyowa kasar asarar da aka kiyasta cewar ta kai ganga miliyan 701.48 tun a shekarar 2009, lokacin da NEITI ta fara bin diddigin asarar da aka yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG