Cutar amai da gudawa ta bula a jihar Neja har ta kama sama da mutane 30 a garin Sabon Wuse, da ke karamar hukumar Tafa a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Anambra, Dr. Lawrence Ikeakor, yace duk da cewa ba a samu rahoton Polio ko guda daya a jihar ba, ba zasu yi sakaci har cutar ta sake bullowa ba.
Shaihin malamin yace ya kamata a kawar da mugun tunani a kyale yara su samu maganin rigakafin wannan muguwar cuta
Kungiyar bada taimako, Catholic Relief Services (CRS), wadda take shugabar karbar taimako na kawar da cutar cizon sauro a Niger, zata kara yada aiyyukanta na kawar da cutar cizon sauro, da gwaji da kuma bada magunguna.
Nijeriya na cikin kasashen duniya dake fama da cututtuka da dama. Ko da yake Nijeriya tana kimanin kashi biyu na yawan mutanen duniya, kasar na dauke da kashi 13 na yawan mutuwar yara a duniya, bisaga kiyashin kungiyoyin mutuwar yara kasan shekara biyar na Majalisar Lafiya ta Duniya na 2013.
Fiye da shekaru 60, yawancin hukumomin lafiya sunyi gargadin amfani da kitsen naman dabbobi cewa yana kawo cutar zuciya da kuma dole a rage shi daga abinci na zuciya. Amma bisaga wani sabon bincike da aka baiyyana a maganin JAMA, cewa sikari shine ainihin abinda ke kawo cutar zuciya ba kishen naman dabbobi ba.
Bankin duniya ya baiyyana kyautan kudi dala miliyan $150 ga gwamnatin tarayya domin inganta sashin lafiyar jihohin Nijeriya, wanda ya kunshi karin taimakon dala miliyan $20 daga gwamnatin kasar Birtaniya.
Ambasadon Amurka a Nijeriya, Mr. James Entwistle, yace gwamnatin tarayyar Amurka ta kashe fiye da dala $3.6 a yaki kan cutar kanjamau a kasar Nijeriya cikin shekaru 10.
Rigakafi wani tsari ne wada ake amfani da shi domin kare mai lafiya daga kamuwa da cuta. Akan fara tun daga ranar da aka haifi yaro. Ya kamata bayan wankan haihuwa da sauran su, a ba yaro dukan alurai da ya kamata, kamar aluran ciwon shan inna da sauransu.
An kaddamar da zagaye na biyu na aikin bayar da rigakafin cutar Polio na wannan shekarar a masarautar Lapai
Ganin irin yadda iyayen yara suke kin kawo yaran su zuwa asibiti domin yi masu rigakafi, likitoci a Maradi ta jamhuriyar Nijar sun dau wani sabon mataki na ganin ana yiwa yara rigakafi.
Jihar Maradi ta jimhuriyar Nijar ta bi sahun sauran jihohi a kasar wajen gudanar da bukin ranar kutare ta duniya wadda ake yi a ranar 25 ga watan daya na kowacce shekara.
Domin Kari