Rahotoni daga jihar Neja na nuna cewa mutane 7 sun halaka da wannan cuta, amma hukumomin kiwon lafiya na jihar sun ce mutane biyu ne cutar ta kashe. Mutanen garin Sabon Wuse da aka samu aka yi magana da su sun ce wanan al'amarin ya tayar masu da hankali kwarai.
Hukumomin kiwon lafiya a jihar Neja sun ce rashin tsabta da rashin ruwan sha mai kyau shine ya kawo bullar wanan cutar a wannan yankin.
Wani babban jami'i mai kula da sashen cututuka na ma'aikatar lafiya a jihar, Mohammed Kudu Buhari, ya bayyana cewa sun je sun je Sabon Wuse kuma sun iske mutum 36 dake fama da cutar kuma mutum 2 suka rasa ran su.
Buhari ya ce sun kai gudumuwa daga gwamnatin Neja, ga mutane masu fama da wanan cutar, da kuma magungunan da jama'a zasu sha domin kiyaye kansu daga kamuwa da cutar.
Ga Mustafa Nasiru Batsari da karin bayani.