In har an bari ya makara ba a yiwa jariri alluran da ya kamata ba, kar ya kai sati ba a bada wadanan rigakafi ba.
Ya kamata a bama dan jariri rigakafi yada ya kamata saboda jikin yaro yana da rauni akan ainihin garkuwan jikinsa. A wanan lokacin ne ya kamata a fara yi mashi rigakafi hawa hawa har lokacin da yaron zai kai wata tara.
A wanan lokaci, rigakafin da za'a bayar sun hada da na tarin fuka, ciwon shan inna, ciwon hanta (hepatitis), kyanda, bakon dauro, da sauransu.
Ya kamata kafin jariri ya kai wata tara za a tabatar an bada duk wadanan aluran rigakafin.
Ga karin bayani.