Wannan aikin shiri ne na shekara biyar wanda zai yi aiki a jihohi uku na Adamawa, Ondo da Nasarawa. Manufar shirin shine ya kara kewaye mahimman sashin lafiya kuma ya kara karfafa su tawurin hanyoyin taimako na kwarai.
Yayinda take jawabi ga ‘yan jaridu a wurin kaddamar wa a Abuja, wakilin Bankin Duniya, Marie-Francoise Marie-Nelly, tace, "wannan aikin ya sami taimakon dala miliyan $150 daga wani kamfani IDA, da kuma dala miliyan $20 daga Burtaniya mai suna HRITF .”
Musamman, ta baiyyana cewa wannan aikin na kokarin kara kayayyakin aiki da kayan lura da mata masu ciki da yara, kiyaye lafiyar haihuwa da kauda cututtuka musamman a tsakanin talakawa a asibitocin gwamnati na jihohin Adamawa, Nasarawa da Ondo.
An gudanar da wannan aikin a karkashin ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayya (NPHCDA), kuma ma’aikatar lafiya ta kasa ita ke jagorantar aikin.
Lokacin jawabinsa awannan taron, ministan lafiya, Prof Onyebuchi Chukwu ya baiyyana cewa, “Duk abinda gwamnatin tarayya tayi a sashin jama’a, kamar sashin lafiya da ilimi, idan ba tare da hadin kan gwamnatin jihohi da kananan hukumomi ba, ba zamu samu cin gaba ba.”
Yace yawan aikin aiwatarwa a sashin lafiya yau yana kan kananan hukumomi da jihohi ne.
Duk da haka, ministan, ya kira ga bukatar jihohin da aka yi amfani dasu domin gwajin wannan aiki, su kara karfi.