Wannan yadawar zai yiwu ne a karkashin karin taimakon kudi dala miliyan $18.1 daidai da (EUR miliyan 13.5 ) wanda ungiyar bada taimako ta duniya, Global Fund, ta bayar a watan Agusta 2013.
A cikin kokarin da ake kan kawar da cutar cizon sauro, an kamala shiri domin gidajen maganin sauro da kuma gwajin cutar cizon sauro. An bayana cewa gidajen sauro da ake sauraron zuwansu zasu iso tsakanin watan Mayu da Yuni, inji William Rastetter, wakilin CRS a kasar Nijer. Rastetter ya bayyana cewa za a sayi wasu gidajen maganin sauro guda miliyan 1.65, wanda za’a rarraba a kewayen sashin Tillabery a kudu maso yammacin Nijer.
Sashin ya hada da babban birnin Niamey, inda aka fi fama da cutar cizon sauro a kasar. An kuma yi shirin kara yawan kudin saye da rarraba gidan sauro kusan miliyan 1.2 – wanda gwamnatin Nijer zata saya da kanta – domin sashin Dosso, shima da yake a kudu maso yamma.
Cutar cizon sauro har yanzu tana matsayin jagoran cutar dake kawo mutuwa a Nijer, da ruhoton mutuwa 3,000 daga matsaloli miliyan 2.6 a shekara ta 2012, bisaga wani bayani na jaridan aikin likitoci, Lancet, na Agusta 2013.