Malam Idi Adamu, wani likita a Danja, a jamhuriyar Nijar yayi bayani kan alamun cutar kuturta. Ya bayanna cewa, alamun cutar kuturta dabam suke. Ya ce kuturta tana da tabbuna ga jiki amma banbancin tanbunan kuturta shine ba ya sa kaikayi.
Ya bayanna cewa alamomi kamar ciwon gwuiwa, rashin karfi ga hannu, ko kasala da faso a jikin mutum, sune ke tura mutum ya je wajen likita wanda zai iya ganowa cewa alamomin kuturta ne. Malam Adamu ya kuma ce ana bada maganin cutar kuturta a kyauta ne.
Sarkin kutare a jihar, Malam Salihu Musa ya ce suna neman taimakon gwamnati domin samun abinci.
Ga cikakken rahoton da Shuaibu Mani ya aiko.