Wani binciken mutane fiye da 40,000 ya baiyyana cewa a wadansu yanayi, yawan shan sikari yana kawo kashi 400 na hadarin cutar zuciya. Wannan binciken ya nuna cewa hadarin cutar zuciya yana karuwa idan sikari ya kai kashi 20 na abinda mutum ke sha.
Bisaga masu bincike, wannan sabon binciken na nuna yadda sikari ke kawo raguwar sinadarin dake rage yawan sikari cikin jinni kuma shi ke kara wuta, wanda likitoci yanzu suka sani cewa shine tushen cutar zuciya. Banda wani irin kitse maisuna trans, yawancin kitse basu da hadari.
Wannan ya hada da kitsen Omega-3, man gyada, wanda aka tabbatar ya rage hadarin cutar zuciya fiye da kashi 30 a binciken kwanannan wanda akayi cikin jama’a da yawa.
Ga cikakkiyar gaskiyar: kaloris na sikari yafi kowanne kaloris hadari. Dukan kaloris ba daya suke ba. Wani bincike na kwanannan, na fiye da kasashe 175, ya nuna cewa karuwar kaloris bai kara hadarin Type 2 na ciwon siga ba, amma karuwar sikari yayi sosai.