Da yake jawabi a wajen kaddamar da wannan gangami a masarautarsa, mai martaba sarkin lapai, Alhaji Umaru Bago Tafida, ya roki jama'a su bayar da hadin kai ga ma'aikatan kiwon lafiyar domin a kawar da wannan cuta.
Yace ba kuma za a iya kawar da cutar ta shan inna ba, har sai kowa da kowa ya bayar da hadin kai sosai.
Jami'i mai kula da yaki da cutar Polio a Jihar Neja, Dr. Yabagi Aliyu, yace an bayar da horo mai kyau ga ma'aikatan da zasu gudanar da wannan aiki a bangaren yunkurin tabbatar da samun nasararsa.
Yace kamar yadda suka saba, a wannan karon ma zasu yi kokarin gudanar da aikin rigakafi mai inganci domin taimakawa al'ummar jihar.
Alhaji Ahmed Musa Ibeto, mataimakin gwamnan Jihar neja, kuma shugaban Kwamitin yaki da Polio na Jiha, ya ce akwai wasu sassa da dama na jihar da suke da wahalar kaiwa a saboda su na cikin tsaunuka ne ko kuma dai sai ta ruwa kawai ake iya kaiwa cikinsu. Yace a irin wadannan wurare, zasu yi amfani da dabbobi da kuma kafa domin dai a ga cewa babu wanda aka bari a baya.