Wannan cuta masana suka ce sakacin hukumomin kasar Saudiyya ce ta sa cutar ta yadu.
Gidauniyar Bill Gate dana Dangote sun sa hannu a rajejeniyar hadin gwiwa.
A wani yunkurin kawo karshen cutar shan inna a jihar Neja, daga yanzu duk wanda ya hana a yiwa 'ya'yansa rigakafin cutar zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Darektan hukumar kiwon lafiya matakin farko na Jihar Neja, Dr. Yabagi Aliyu, yace ya zuwa yanzu, alkaluma sun nuna yara fiye da miliyan biyu da rabi suka karbi wannan magani a zagaye na uku na rigakafi a wannan shekara.
Mai Martaba Rilwanu Sulaiman Adamu, ya fada a wani taron da VOA ta shirya cewa kafa dokar tilasta yin rigakafin Polio zata taimaka wajen dakile yaduwarta a cikin jihar.
Kungiyar mai suna Volunteer Community Mobilisers ta ce ta dauki ma’aikatan ne a kananan hukumomin Bauchi da Toro domin bunkasa aikin rigakafin Polio a yankunan
Likiotci sun tabbatar cewa har yanzu maganin kawas da kanjamau ita ce zata kawo karshen cutar. Masana suna kan neman allurar rigakafin cutar saboda banbancin al’adu da sauransu yana rage kokarin kauda wannan cutar.
Hakoran yaran ka zasu iya rubewa idan ba a kula da su ba. Dasashin hakorin yaro bashi da karfi kamar yadda na babban mutum yake – ko sabbin hakoran manya basu da karfi a farin shekarunsu.
Rashin biyan kudaden alwus-alwus ya jawo yajin aikin likitoci a janhuriyar Nijar.
Jakada Nigeria a kasar Guinea ya tabo fannoni daban-daban na abinda ke haddasa cutar Ebola, wanda yakewa jama'a da yawa barazana a yammacin Afirka.
Kimanin mutane tamanin da huidu ne suka mutu sandiyar barkewar zazzabin ebola a kasar Guinea .
Jami'an gwamnatin kasar Mali na binciken rashin lafiyar wasu mutane uku da ake zaton cutar Ebola ce, a jiya Jumm'a ministan lafiyar kasar Mali ya bada sanarwar mutanen uku, a daidai lokacin da kasashen yankin ke fama da bullar mummunar cutar mai kisa.
Domin Kari