Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Hukunta Duk Wanda Ya Hana Rigakafin Shan Inna


Ana ba wasu maganin cutar shan inna
Ana ba wasu maganin cutar shan inna

A wani yunkurin kawo karshen cutar shan inna a jihar Neja, daga yanzu duk wanda ya hana a yiwa 'ya'yansa rigakafin cutar zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Daga yanzu gwamnatin jihar Neja zata hukunta duk wani wanda ya hana a yiwa 'ya'yansa rigakafin cutar shan inna. Wannan cigaba ne da kokarin dakile citar a jihar.

Gawmanatin tace daga yanzu za'a yiwa mutum hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari ko a cishi tarar nera dubu hamsin. Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Isa Ibeto shi ya tabbatar da hakan lokacin da ya kaddamar da aikin bayar da allurar rigakafin cutar karo na hudu a cikin wannan shekarar. Gwamnatin tace a yanzu babu wani dalilin rashin amincewa da allurar rigakafin. Yace ko ta addini ne ka fito baka da madafa. Idan kuma ta al'ada ce babu hujja. Dalili ke nan da majalisar dokokin jihar Neja ta fito da dokar.

Babu shakka gwamnatin jihar ta dauki matakin babu sani babu sabo akan kawar da cutar shan inna. Gwamnatin ta kara da cewa daga yanu duk yaron da bai nuna takardar sheidar samun allurar rigakafi ba, ba za'a daukeshi a kowace makaranta ba a jihar kamar yadda kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar ta sanar Hajiya Hadiza Abdullahi. Tace an dauki matakin ne domin kare yaran da yaran anguwa domin wani zubin iyaye su kan yi karya.

A wannan karon hukumomin kiwon lafiya sun ce sun dauki matakai domin tabbatar da samun cin nasara a wannan zagayen da za'a fara ranar Asabar mai zuwa har zuwa Litinin din makon gobe. Dr Yabagi Aliyu daraktan kiwon lafiya matakin farko yace sun dauki matakan ne domin tabbatar da an ci nasara.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG