Sarkin na Bauchi, ya yi wannan kiran ne a cikin kasidar da Dan Amar na Bauchi, Alhaji Hassan Bayero, ya gabatar a madadinsa a wurin taron yaki da cutar Polio wanda Muryar Amurka da kuma Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu yaduwa ta Amurka suka shirya a Bauchi.
Yace yin hakan zai tilasta ma iyayen dake kin yarda su samarwa da ‘ya’yansu wannan kariya ta rigakafin su karbi wannan magani mai muhimmanci.
Yace koda yake an samu raguwar wannan cuta sosai, akwai bukatar kafa dokar da zata iya hukumta iyayen da suka ki ba ‘ya;’yansu kariya.
Amma kuma sarkin na Bauchi yayi kiran da a daina yin amfani da yaran da shekarunsu bas u kai na balaga ba a matsayin masu aikin bayar da rigakafin, abimnda a can baya ya sa wasu iyaye suka ki yarda a diga ma ‘ya’yansu wannan maganin.