An yi kira ga gwamnatoci da ma’aikatun lafiya a Najeriya da suyi himma wajen kiwon Lafiya a Najeriya.
Faman da Nijeriya take ciki da cutar tarin fuka ya fi yadda ake sammani. An bincika cewa zai zama kamar sau uku fiye da yadda kungiyar lafiya ta duniya ta fadi da kuma sau biyar fiye da wadda akayi rahoto a kungiyar kiyaye cutar tarin fuka da kuturta, inji ministan lafiya na jiha, Dr Khaliru Alhassan.
Gwamnatin kasar Guinea na kokawar neman shan kan bazuwar kwayar mummunar cutar Ebola mai kisa, a yayin da makwafciyar ta , kasar Senegal ta rufe kan iyakokin ta na kudanci da suka hada su.
Kwayar cutar Ebola, wadda ya barke a Afrika tun shekara ta 1976, daya ne daga cikin su mumunar kwayoyin cututuka da aka sani.
Ilimin tsabtar abinci na nufin tsabtar da ake dauka wajen shirya abinci da kayan girki.
Lokacin da bakon dauro ya fara fitowa a karni na 10 cikin rubuce rubucen mai magani na Persia, mutane sun yarda cewa ana samun shi daga uwa zuwa yaro ne.
Kungiyar lafiya ta duniya tana kara kira ga mutane su rage yawan sikarin da suke sha.
Masanan kimiyya a kasar Amurka suna kira ga wani magani mai inganci da zai iya kai ga warkar da cutar kanjamau.
Sakataren kungiyara majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon yace za’a sa kokari wajen inganta lafiyar mata da yara tawurin wani sabon shiri wanda za’a raba ra’ayoyi da nasarori cikin kasashe masu tasowa.
Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya baiyyana damuwar shi cewa Nijeriya tayi baya wajen maganar lafiya ta duniya baki daya.
Likitoci sun gano kwayar cutar Ebola a kasar Guinea, lokacin da wata irin zazzafar masassara mai sa zubar jini ta fatar jiki ta barke ta kuma halaka mutane 34 a kalla a kasar.
A shekaru uku masu zuwa, kamfanin hada magunguna na AstraZeneca, zai sa jarin Naira miliyan 48 a binciken magunguna a Nijeriya domin ya gina yawan magunguna da kuma taimakon masana yin bincike.
Domin Kari