Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ce cutar nan mai kama da mura, wacce ta zaburo cikin watan Afrilu a kasar Saudiyya yanzu ta lafa, duk da haka hukumar tace her yanzu da sauran aiki wajen shawo kan cutar.
Cutar da ake kira MERS a takaice cikin harshen turanci ta kama mutane fiye da 700 a duk fadin duniya dukkansu sun kamu da cutar ta wani dalili mai nasaba da kasar Saudiyya.
Cutar mai shigen mura ta kuma kashe mutane fiye da 250 a fadin duniya.
Wannan cuta tuni ta yadu musamman a kasashe da suke yankin gabas ta tsakiya kamar su Jordan, Iran da Aljeriya, dukkan wadanda suka kamu a da cutar daga wadanan kasashe mutane ne da suka kai ziyara kasar Saudi Arabiya domin ibada.
Ko anan Amurka wasu mutane biyu masu aikin kiwon lafiya a kasar Saudi Arabia wadanda suka dawo nan Amurka sun kamu d a cutar. Mutanen 'yan asalin jihohin Florida da Indiana ne.
Dr. Hassan Bashir Jibrin likita ne mai zaman kansa a jihar Florida dake nan Amurka yayi karin haske dangane da wannan cuta.
Ga Kashi na daya.