Ciwon hakori zai iya damun cin abinci, barchi da kuma raya ilimi a mahimman lokaci da yara suke girma. Rubewar hakorin kananan yara kuma yana jawo damuwan hakori da zai zauna har idan yara sunyi girma. Hakora marasa pasali babu dadin gani.
Domin kare wadannan damuwar, likitoci sun bada shawarar cewa yara su goge bakinsu akalla sau biyu a yini da man goge baki; na farko da safe da kuma bayan an ci abinci da dare.
Wannan bazai taimaka wanke kwayar cutar ba ne kawai, amma man goge baki yana taimakon karfafa hakokara da kuma kiyaye su daga rubewa.