Shugaban kungiyar, Alhaji Auta Kawu, ya fada lahadin nan a Bauchi cewa sun dauki wadannan ‘yan agaji ne a yankunan kananan hukumomin Bauchi da Toro, kuma a yanzu haka sun a cikin masu aikinrigakafi a wadannan yankuna biyu.
Ya kara da cewa wadannan ‘yan agajin suna kuma ilmantar da jama’a kan muhimmancin awun ciki ga mata masu juna, da kuma sauran alluran rigakafin da ake ba yara.
Yace irin matakan da kungiyarsa tare da wasu hukumomin suka dauka sun kai ga taimakawa wajen rage yaduwar cutar shan inna ta Polio, wadda aka samu yara biyar da suka kamu da ita a shekarar 2013, amma a watanni uku na farkon wannan shekara ba a samu ko guda daya ba.