Kasar Kamaru na yaki da safarar koko da auduga da kuma sauran kayan amfanin gona zuwa Najeriya, inda ta haramta cinikaya na wucin gadi bisa ka’ida na tsawon dan wani lokaci.
A kasar Kamaru hankalin mutane ya karkata kan matsalar da ta shafi hamshakin attajiri Alhaji Baba Danfullo, inda gwamnatin Afirka ta Kudu ta kwace kadarorinsa da dama.
Musulmai a yankin Sama Maso Gabashin Ghana, wanda ke kunshe da gundumomi 15, ba za su yi layya a babbar Sallar ban aba kamar yadda sauran Musulmai a fadin duniya za su yi ba, saboda yaduwar cutar Anthrax a dabbobi da ta yi kamari a yankin.
An kashe wasu mutane biyar a ranar Lahadi a lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka kai hari a wasu kauyuka biyu a gundumar Lamu da ke kudu maso gabashin kasar Kenya, in ji ‘yan sanda.
A yayin da yake bitar karshen aiyukan jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki a albarkacin hajin shekarar 1444 da ke dai dai da shekarar mai ladiya ta 2023 shugaban hukumar alhazzan Nijer Commissaire Ibrahim Kaigama, ya tabbatar da cewa an yi nasarar isar da dukkan maniyatan kasar a kan lokaci.
Hukumar da ke sa ido kan kafofin yada labarai ta Kamaru, ta yi barazanar dakatar da gidajen talabijin, musamman na kasashen waje, wadanda ke yada hotunan bidiyo masu nuna alakar auren jinsi daya, dabi’ar da kasar ta haramta.
A jamhuriyar Nijer samfarin sabon taken kasar da majalissar dokoki ta yi na’am da shi a zamanta na ranar alhamis ya haifar da dambarwa a tsakanin al’ummar kasar.
Faduwar fiye da kashi tamanin cikin dari na malaman makaranta a Ghana na jarabawar lasisin koyarwa ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar musamman tsakanin masu ruwa da tsaki inda wasu ke ganin wannan babban barazana ce ga tsaron kasar.
Majalissar dokokin Jamhuriyar Nijer ta yi wa ayar farko ta kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska da nufin samun sukunin shigar da sabon taken kasar da zai maye gurbin wanda ake amfani da shi tun a jajibirin samun ‘yancin kan kasar daga turawan mulkin mallaka.
Kamaru ta hana fitar da koko zuwa Najeriya, sakamakon kara da manoma koko a Kamaru su ka kai musamman a yakin kudu maso yammacin Kamaru.
Binciken ya nuna cewa Dakta Bawumia ya samu kashi 34.8% na kuri'u, sai tsohon ministan kasuwanci da masana’antu, Alan Kyerematen da ya samu kashi 27.9%, sannan Kennedy Agyapong ya samu kashi 12.5%.
Rundunar sojin ruwan Ghana ta karbi jiragen ruwa guda biyu masu gudu daga kasar Amurka, don taimakawa wajen kara inganta tsaro a cikin tekunta, a wani biki da aka gudanar a tashar jiragen ruwa ta Takoradi da ke yankin tsakiya.
Domin Kari