Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Ruwan Ghana Sun Sami Gudunmawar Jiragen Ruwa Biyu Daga Amurka



Sojin Ruwan Ghana Sun Samu Gudunmawar Jiragen Ruwa Biyu Daga Amurka Don Karin Tsaro
Sojin Ruwan Ghana Sun Samu Gudunmawar Jiragen Ruwa Biyu Daga Amurka Don Karin Tsaro

Rundunar sojin ruwan Ghana ta karbi jiragen ruwa guda biyu masu gudu daga kasar Amurka, don taimakawa wajen kara inganta tsaro a cikin tekunta, a wani biki da aka gudanar a tashar jiragen ruwa ta Takoradi da ke yankin tsakiya.

ACCRA, GHANA: Jiragen guda biyu sun iso tashar jiragen ruwan Takoradi a cikin katafaren jirgin ruwa mai suna Ocean Giant, kuma kowanensu na da karfin gudun Knots 25.

Babban hafsan sojin ruwan Amurka a Ghana, Kwamanda Carlton McClain, shi ne ya mika jiragen ruwa guda biyu ga Ghana a madadin Amurka, yayin da babban kwamandan Rundunar Sojin Ruwa na yankin Yamma, Commodore Emmanuel Kwafo, ya karbi jiragen ruwan a madadin gwamnatin Ghana.

A jawabinsa, Kwamanda Carlton McClain, ya ce sojojin ruwan Ghana na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron teku a mashigin tekun Guinea, don haka jiragen ruwan za su karfafawa Ghana a aikin tsaron tekun yankin.

Sojin Ruwan Ghana Sun Samu Gudunmawar Jiragen Ruwa Biyu Daga Amurka Don Karin Tsaro
Sojin Ruwan Ghana Sun Samu Gudunmawar Jiragen Ruwa Biyu Daga Amurka Don Karin Tsaro

Ya kara da cewa, "Ghana ita ce kawarmu mafi mahimmanci, musamman a fannin tsaro na yankin mashigin Guinea da kuma Yammacin Afirka. Yankin mashigin Guinea yana da mahimmanci ta fuskar kasuwanci, kuma muna farin cikin taimakawa Ghana a wannan kawancen.”

Commodore Emmanuel Kwafo, yayin da ya ke mika godiya ga gwamnatin Amurka kan jiragen, ya ce hakan zai kara inganta tsaro a yankin yamma mai nisa da kuma gabashin tekun Ghana.

Commodore Kwafo ya ce, “Ina so in mika godiyarmu ga gwamnati da jama'ar Amurka bisa ga wannan karimcin. Za mu kira daya GNS AFLAO dayan kuma GNS HALF ASSINI”. Ya ce, jiragen za su iya kasancewa a cikin teku na kusan kwanaki uku, don haka suna da kyau sosai kuma za su amfani kasar Ghana.

Mai sharhi kan harkokin tsaro Al-Hassan Bello, ya bayyanawa Muryar Amurka yadda wadannan jiragen ruwan za su taimaka wajen tsaron gabar tekun Ghana da mashigin Guinea, da kuma siyasar da ke tattare da shi.

Ghana Ta Samu Gudunmawar Jiragen Ruwa Biyu Daga Amurka Don Karin Tsaro
Ghana Ta Samu Gudunmawar Jiragen Ruwa Biyu Daga Amurka Don Karin Tsaro

Yace, baya ga kara dankon alaka tsakanin kasar Amurka da Ghana, cece-kuce tsakanin kasar Amurka da Rasha da China kan kasuwanci ya yi tasiri kwarai wajen ire-iren wadannan taimakon ga Ghana, idan aka yi la’akari da yadda China ta zuba hannun jari a Afirka. Yace, irin wannan taimakon zai karawa Amurka matsayi a idon gwamnatocin Afirka.

Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Mustapha Madugu ya jaddada muhimmancin jiragen ga tsaron tekun Ghana.

Ya ce “Sojin ruwan Ghana za su yi amfani da jiragen wajen kare iyakokin Ghana, da hana ‘yan fasa kwaurin miyagun kwayoyin da makamai, haka kuma za su taimaka wajen aikin ceto, idan kwale-kwale ya nitse”.

A ranar 25 ga watar Afrilun 2023 shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya kira taron kasashen yankin mashigin Guinea domin tattauna dabarun karfafa tsaro kan laifukan da suka shafi teku da suka addabi yankin.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:

 Sojin Ruwan Ghana Sun Samu Gudunmawar Jiragen Ruwa Biyu Daga Amurka Don Karin Tsaro.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG