YAOUNDÉ, CAMEROON - Danfullo ya lashi takobi kwato hakkinsa ta hanyar shari’a da nufin kai karar kamfonin da Afirka ta Kudu ke da hannun jari a cikinsu kamar MTN da CHOCOCAM.
Wannan matsalar ta samo asali ne a shekarar 2020 sa'adda Babban Bankin Afirka ta Kudu (FNB) ya sayar da kadarorin Ahmadou Baba Danfullo da ke kasar. A cewar bankin, wannan babban dan kasuwan kasar Kamaru ya kasa biyan bashi da ake bin sa tun shekarar 2019.
Baba Danfullo ya musanta zargin, kuma ya yi magana kan wata karya da ya ce na da nufin kwace masa kadarorinsa ta hannun kamfaninsa mai suna Bestinver, wanda aka fi sani ta bangaren gidaje a kasar Afirka ta Kudu.
Karar tasa ba ta yi nasara ba a kotuna kan matakin da bankin FNB ya dauka a Afirka ta kudu.
Daga nan ne Baba Danfullo ya juya ga gidajen shari’a na Kamaru, tare da manufar karbe asusun ajiyar banki na MTN Broadband Telecoms, Mobil Money Corporation da Chococam domin kwato kudaden da bankin First National Bank ya karkatar.
A kan haka Baba Danfullo ya fusata da MTN Kamaru da Chococam, domin su rassa ne na kamfanin Public Investment Corporate (PIC), wanda kuma ke da hannun jari a bankin na First National Bank.
Daraktotin MTN Cameroon sun ce “sabanin abin da ake zargin mu da shi, daga ma’aikacin banki na Bestinver har kamfanin Public Investment Corporation, ba su da hannun jari a kamfanin MTN Kamaru”
Har ila yau, sun kara da cewa “ba mu fahimci yadda za,a bayar da umarnin karbe asusun ajiyar bankin na MTN Kamaru ba, alhali ba'a alakanta su da Bestinver ko Danfullo ba, har ma da ma ma’aikacin bankinsu na Afirka ta Kudu”
Ahmadou Baba Danfoullo na fatar a kwato masa hakkin sa na kudi kimamin biliyan 259 na FCFA, a karshen wannan shari’a, a kan wadannan rassan Afirka ta Kudu a Kamaru.
Saurari cikakken rahoto daga Mohamed Bachir Ladan: