Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalissar Dokokin Kasa Ta Amince Nijer Ta Canza Takenta


Taron Majalissar Dokokin Nijer
Taron Majalissar Dokokin Nijer

Majalissar dokokin Jamhuriyar Nijer ta yi wa ayar farko ta kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska da nufin samun sukunin shigar da sabon taken kasar da zai maye gurbin wanda ake amfani  da shi tun a jajibirin samun ‘yancin kan kasar  daga turawan mulkin mallaka. 

Bayan tafka mahawwara Majalisar ta kwaskware ayar doka ta farko ta kundin tsarin mulkin kasa wace ke bayani kan taken Nijer. Daukacin ‘ayan majalisa 149 da suka halarci zaman ne suka yi na’am da gyaran fuskar abinda ke nufin wakilan al’ummar ta Nijer sun amince da sabon samfarin taken na kasa mai sunan L’honneur de la Patire wato mutuncin kasa.

Majalissar Dokokin Nijer
Majalissar Dokokin Nijer

Ministan al’adu Mohamed Hamid ya yaba da hadin kan ‘yan majalisar suka bai wa gwamnati a sabuwar tafiyar ta sa gaba.

Majalissar Dokokin Nijer
Majalissar Dokokin Nijer

Koda yake sun kada kuria’r amincewa da sabon taken na kasa ‘yan adawa a ta bakin dan Majalisa Souamana Sanda na cewa ba shi ne abinda ke gaban talakawan Nijer ba a yau idan aka yi la'akari da tarin matsalolin da ake fuskanta a fannoni da dama.

A nan gaba kadan shugaban kasa Mohamed Bazoum zai saka hannu kan takardar da za ta soke tsohon taken La Nigerienne don kaddamar da sabon taken da aka yi wa suna l’honneur de la Patrie.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG