Wani sabon bincike da kamfanin binciken ra’ayin jama'a mai zaman kansa a Ghana, Global InfoAnalytics, da kafar yada labarai ta Citi TV/FM suka gudanar a tsakanin wakilan jam'iyyar NPP mai mulki, ya nuna cewa Mataimakin shugaban kasa, Dakta Mahamudu Bawumia ne a kan gaba a zaben fidda gwani na dan takarar zama shugaban kasa na jam’iyyar da ke tafe, sai dai zai iya faduwa a zaben idan an shiga zagaye na biyu.
Binciken ya nuna cewa, Dakta Bawumia ya samu kashi 34.8% na kuri'u, sai tsohon ministan kasuwanci da masana’antu, Alan Kyerematen mai kashi 27.9%, sannan sai Kennedy Agyapong mai kashi 12.5%.
Sauran 'yan takarar dai sun samu kasa da kashi 1% na kuri'un da aka kada, yayin da kashi 8.9% suka ki bayyana wanda suke son kadawa kuri'a, sai kashi 15.10% har yanzu ba su yanke hukuncin wanda za su zaba ba.
Babban darektan kamfanin InfoAnalytics, kamfanin da ya gudanar da binciken, Mussa Dankwa, ya nuna cewa zaben zai iya kaiwa ga zagaye na biyu, kuma idan hakan ya faru, Alan Kyeremanten zai iya yin nasara kan Dakta Bawumia. Yace, idan wadanda ba su yanke hukunci ba, da kuma wadanda suka ki fadar wanda za su zaba suka canja matsayinsu, to za a iya zuwa zagaye na biyu. Kuma idan an je zagaye na biyu, sauran mabiyan ‘yan takaran za su kada wa Alan Kyeremanten ne, maimakon Dakta Bawumia, domin addininsu da yankin da suka fito ya fi dacewa da na Alan ne.
Sai dai mabiya bayan Dakta Bawumia ba su ganin zaben zai kai ga zagaye na biyu, kamar yadda Issaka Ibrahim, mamban tawagar sadarwar jam’iyar NPP, kuma mai goyon bayan Bawumia ya ce. “Kashi 90% na wadanda suka rako Dakta Bawumia ranar da zai mika fom din shiga takara, wakilai ne da za su kada kuri’a. Babu shakka, ba mu tsammanin Dakta zai samu kasa da kashi 70% na k7uri’un da za a kada” in ji Issaka; domin haka, ba za a je zagaye na biyu ba.
Shi kuma Mujeeb Rahman, mamban tawagar yakin neman zaben Alan Kyeremanten, ya ce wadannan wakilan da ba su da wanda za su kadawa kuri’a ba, lallai Alan za su bai wa kuri’unsu. Ya kara da cewa, ba ya tsammanin za a kai ga zagaye na biyu, domin dan takaransa, Alan Kyeremanten ne zai ci.
Sadat Yahaya Baako, mamban tawagar sadarwar jam’iyar NPP yace duk wanda ya lashe zaben fidda gwani na NPP, lallai shi ne zai kafa tarihi na kai jam’iyar ga wa’adin mulki sau uku a jere.
A halin yanzu ‘yan takara 10 sun mika fom din neman shiga takara ga kwamitin tantancewana jam’iyar, kuma za a kada kuri’ar zaben fidda gwanin a ranar 4 ga watan Nuwamban 2023.
Saurari rahoton Idris Abdullah: