Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Biyar A Wani Hari Da Aka Kai A Lardin Lamu Na Kasar Kenya


SOMALIA
SOMALIA

An kashe wasu mutane biyar a ranar Lahadi a lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka kai hari a wasu kauyuka biyu a gundumar Lamu da ke kudu maso gabashin kasar Kenya, in ji ‘yan sanda.

WASHINGTON, D.C. - Maharan sun kuma kona gidaje tare da kuma lalata dukiyoyi.

'Yan sanda sun bayyana lamarin a matsayin "harin ta'addanci," kalmar da suka saba amfani da ita a duk lokacin da kungiyar al-Shabaab ta Somalia mai kishin addinin Islama ta kai wani hari.

Wasu Yan bindiga
Wasu Yan bindiga

Garin Lamu na a kusa da kan iyakar Kenya da Somaliya kuma mayakan kungiyar al Shabaab sukan kai hare-hare a yankin a zaman wani kokari na matsa wa hukumomin Kenya lamba su janye sojojin kasar daga Somaliya, inda suke taka rawa a rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa dake kare gwamnatin tsakiyar kasar.

‘Yan sanda sun ce wasu mahara ne suka kai hari kan kauyukan Salama da Juhudi da sanyin safiyar Lahadi.

Wasu Yan Bindiga
Wasu Yan Bindiga

An daure wani dattijo mai shekaru 60 da igiya "aka kuma yanka wuyan shi da wuka, sannan aka kona gidansa da kayansa kurmus". Hakazalika aka kashe wasu mutane uku ta wannan hanyar yayin da aka harbe mutum na biyar.

An kona gidajen wadanda aka kashe da kuma na wasu mazauna garin a harin, sannan maharan suka gudu zuwa wani daji da ke kusa da wurin, in ji ‘yan sanda.

Kungiyar al Qaeda da ke da alaka da al Shabaab ta kwashe shekaru tana fafatawa a Somalia domin neman hambarar da gwamnatin tsakiya ta kasar da kuma kafa gwamnatin shari'ar musulunci mai tsanani.

-Reuters

XS
SM
MD
LG