Cikin sanarwar da ta fitar hukumar ta CNC, ta bayyana lura da yawaitar shirye-shiryen da ke kokarin yada dabi’ar ta masu auren jinsi daya, musamman wadanda ake nunawa ta hanyar amfani da zane ko ‘yar tsana da aka fi sani da ‘Cartoon’ a turance.
Hukumar sa ido kan kafafen yada labarai ta bukaci dukkanin tashoshin da ke tallata shirye-shiryen da su gaggauta janye su, ko kuma su hadu da fushin gwamnati.
Barista Mohaman Hamza ya shaidawa wa Muryar Amurka cewa alakar auren jinsi guda haramtacciya ce a Kamaru, inda ake zartas da hukuncin daurin watanni 6 zuwa shekaru 5 a gidan Yari. Sai dai Kamaru ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai taken "Protocole de Maputo". Wannan dokar kasa da kasa kuwa tayi fishe kan dokar Kasar Kamaru.
Har zuwa wannan lokacin dai ba a bayyana sunayen kafofin talabijin din da ke tallata shirye-shiryen na masu auren jinsi ba, duk da cewar babu bukatar wallafa sunayen kafafen domin adadin tashohin na da dama.
Saurari rahoton Mohamed Ladan a sauti: