A yayin da wasu ke nuna gamsuwa da sabon taken wasu na danganta shi da salon wakokin da ake rera wa jam’iyar PNDS mai mulki saboda haka suka ce da sake.
Kiraye kirayen jama’ar Nijer kan bukatar sauye sauye game da abubuwa da dama da aka gada daga turawan Mulkin mallaka, ya sa mahukuntan kasar daukan matakan da suka bada damar kirkiro da sabon taken, wanda tuni majalissar dokokin kasa ta yi na’am da shi da kyaukyawan rinjaye, lamarin da ya sa ‘yan kasar fara bayyana matsayinsu a kai. Shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou na mai gamsuwa da wannan yunkuri.
Haka shi ma Jigo a kungiyar Tournons La Page Moudi Moussa ya yaba da matakin watsi da tsohon taken.
Salon da aka rera sabon taken ya haifar da cece kuce a tsakanin ‘yan kasa sakamakon lura da yadda abin ke kama da wasu wakokin jam’iyar PNDS mai mulki, a ra’ayin Moudi Moussa girman wannan dambarwa ya kai matsayin da za a shirya zaben raba gardama.
To sai dai fa Nassirou Saidou na ganin bakin alkalami ya rigai ya bushe, illa iyaka a bar kowa ya ci gaba da morar ‘yancinsa na dan kasa.
A shekarar 1961 ne aka tsara wa Nijer takenta na farko da aka yi wa suna La Nigerienne, to sai dai sabon yanayin tafiyar siyasar duniyar da ake ciki a ‘yan shekarun nan ya sa ‘yan kasar suka matsa lamba akan bukatar ganin an jefar da taken da wasu ke dauka a matsayin daya daga cikin igiyoyin da Faransa ke amfani da su don ci gaba da zame wa kasashen da ta yi wa mulkin mallaka tamkar rakumi da akala.
Saurari rahoton a sauti: