Sai dai mambobin bangaren 'yan adawa a kasar irinsu Tahirou Guimba, na ganin alamun an yi zaben tumun dare.
A yayinda ake bukin tunawa da Ranar ‘Yancin Aikin Jarida a yau Talata, 3 ga watan Mayu a ko ina a sassan duniya, cibiyar ‘yan jarida a Jamhuriyar Nijer ta yi bitar halin da aikin jarida ke ciki a kasar mai fama da matsalolin tsaro, da na tattalin arziki.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fara ziyarar aiki a jamhuriyar Nijer, inda ya gana da hukumomin kasar a yau Litinin 2 ga watan Mayu kafin ya isa gundumar Ouallam a gobe Talata don ganawa da mutanen da matsalar tsaro ta tilasta masu tserewa daga garuruwansu na asali.
Kwamitin da ya jagoranci babban taron zaman lafiya da hadin kan al’umomin jihar Tilabery ya damka rahoton karshen wannan taro ga shugaban kasa Mohamed Bazoum domin sanar da shi mahimman shawarwarin da aka tsayar.
Da alamar kwalliya na biyan kudin sabula a hadin gwiwar da sojojin Janhuriyar Nijer ke yi da na Burkina Faso wajen yaki da 'yan ta'adda a kan iyakokin kasashen biyu.
Majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta amince wa gwamnatin kasar akan shirinta na bai wa wasu kasashen ketare izinin kafa sansanin soja a matsayin wani bangare na karfafa matakan yaki da kungiyoyin ta’addancin da suka addabi yankin sahel.
A jamhuriyar Nijar kotun dake kula da yadda aka kashe kudaden gwamnati ta fitar da rahoton binciken da ta gudanar a fannoni da dama na wasu ofisoshin hukuma da kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnatin kasar.
A ranar Juma’a 22 ga watan Afrilu majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar, za ta tattauna bukatar bai wa sojojin ketare izinin girke dakaru a kasar a ci gaba da karfafa matakan yaki da ta’addanci.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun cafke ministan watsa labaran kasar Mahamadou Zada saboda zarginsa da yin rub da ciki akan dubban miliyoyin cfa a zamanin da ya ke rike da mukamin babban Darektan kamfanin dillancin ma’adanai SOPAMIN.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta aika wa majalisar dokoki takardar bukatar gyaran fuska wa tsarin manufofinta a fannin huldar soja da kasashen waje a ci gaba da neman hanyoyin tunkarar kalubalen tsaron da ke gaban Nijer.
A Jamhuriyar Nijer bayan da a yammacin jiya, 15 ga watan Afrilu, Kirista suka yi addu’oin raya Babbar Juma’a da ke daidai da zagayowar ranar mutuwar Yesu Almasihu, a ci gaba da shagulgulan bukukuwan Ista na shirin gudanar da taron sujjada a gobe Lahadi.
A Jamhuriyar Nijar, mabiya addinin Kirista na shirye shiryen gudanar da shagulgulan sallar Easter a karshen makon nan inda a yammacin wannan Juma’a za su hallara majami’u domin addu’oi'n tunawa da ranar mutuwar Annabi Isa Alaihissalam.
Maharan sun fara ne da harba rokoki akan wasu motocin ‘yan sanda biyu kirar VAB masu dauke da manyan bindigogi kafin su bude wuta akan ‘yan sandan dake aiki a wannan tasha.
Hukumomin Jamhuriyar Nijer sun cafke tsohon Ministan Cikin Gida bugo da kari tsohon Jakadan kasar a Chadi, Ousman Cisse, saboda zarginsa da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 31 ga watan Maris na 2021.
A jamhuriyar Nijer kungiyar masu noman zamani ta kaddamar da shirin samar da wadatar irin shuka a yankunan karkara da nufin shafe hawayen manoma a wannan fanni inda a ‘yan shekarun nan illolin canjin yanayi ke haddasa koma bayan amfanin da ake samu a karshen damana.
Duk da cewa magoya bayansa na ganin ya zo da sabon salon mulkin da ba a taba ganin irinsa ba a tsawon shekaru sama da 30 na dimokradiyar kasar, bangaren 'yan adawar na ganin shugaban ya gaza.
Domin Kari