An shiga wuni na biyu na taron kare muhalli da sauyin yanayi wato COP 15 dake gudana a birnin Abidjan na kasar Cote d’ivoire (Ivory Coast), inda a wannan karon ake nazarin hanyoyin da za a bullo wa kwararowar hamada a sassa daban daban na duniya irinsu jamhuriyar Nijer.
Kwararowar hamada da zaizayar kasa abu ne da ke fayyace illolin dake da nasaba da canjin yanayi, wadanda ko baya ga matsanancin zafi, al’amarin kan tayar da guguwa da kura, abin da kuma ke shafar ayyukan noma da kiwo a kasashen Sahel, kamar yadda abin yake a yanzu haka a jamhuriyar Nijer. Shugaban kungiyar plate forme paysanne, Djibo Bagna na fayyace girman matsalolin da canjin yanayi ya haddasa wa sha’anin noma da kiwo a wannan kasa.
Gurgusowar hamada kan mamaye sama da hectare 100000 na kasar noma da kiwo a kowace shekara a jamhuriyar Nijer abinda a dai gefe ke haddasa kafewar albarkatun ruwa inji masana a kasar da fiye da kashi 80 daga cikin 100 na jama'arta ke dogara da noma da kiwo, dalili kenan hukumomi suka tashi tsaye don tunkarar wannan la’amari inji Dr Haboubacar Manzo mashawarci a fadar shugaban kasa.
Lura da yadda wannan matsala ke haddasa fari a kasar da aka fi maida hankali akan noman damana ya sa masana suka dukufa wajen bincike don samar da irin abinci da na ciyawar dabobi wadanda ba sa bukatar dogon lokaci. Pr Falalou jami’i ne a cibiyar nazari da bincike ta ICRISAT, kuma ya yi karin haske a hirarmu.
Kashi 2 daga cikin 3 (sulusi biyu) na fadin kasar Nijer yanki ne da hamada ta yi wa mamaya, domin dakatar da kwararowar wannan bala’i gwamnatin kasar ta bullo da ayyukan gayyar dashen itatuwa ta shekara shekara yayin da a daya bangare hukumomi da kungiyoyi kan shirya ayyukan farfado da kasar noma da kiwo to amma duk da haka matsalar na nan gidan jiya sanadiyar dabi’ar sare itace ba ji ba gani a wani lokacin da tururin injinan cikin gida da na waje ke janyo dumamar yanayi da gurbacewar iska.
Saurari rahoton Suleiman Barma: