Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Rangadi A Nijer


Ziyarar Antonio Guterres Nijer
Ziyarar Antonio Guterres Nijer

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fara ziyarar aiki a jamhuriyar Nijer, inda ya gana da hukumomin kasar a yau Litinin 2 ga watan Mayu kafin ya isa gundumar Ouallam a gobe Talata don ganawa da mutanen da matsalar tsaro ta tilasta masu tserewa daga garuruwansu na asali.

Niamey, Niger - Tattaunawar keke da keke ta kusan awa daya aka yi a tsakanin jami’an tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta hukumomin Nijer a fadar shugaban kasa albarkacin rangadin na Antonio Guterres kafin daga bisani su yi wa manema labarai karin bayani game da makasudin wannan ziyara.

“Zaman lafiya da kwanciyar hankali, da samar da walwala a Nijer da baki dayan yankin Sahel wani abu ne da Majalisar Dinkin Duniya ke dauka da muhimmanci kuma ina jinjina wa jami’an tsaronku saboda jajircewarsu a kulliyaumin a yaki da ta’addanci da masu tsauraran ra’ayin addini, a cewar Guterres.

Ya kara da cewa, na yi fafitika sosai don ganin an bai wa rundunar G5-Sahel damar shiga karkashin kudirin Majaliasr Dinkin Duniya ta yadda zai zama wajibi a dauki dawainiyar kudaden da za ta yi amfani da su wajen gudanar da yaki da kungiyoyin ta’addanci da suka addabi yankin Sahel, sai dai haka ta ba ta cimma ruwa ba.

Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya bayyana girman matsalolin da aika aikar ‘yan ta’adda ta haddasa wa kasar.

Yana mai cewa “ta’addanci ya tilasta mana ninka yawan sabbin sojoji da muka saba dauka muna ba su horon da ya zarce wanda muka saba basu kafin zuwan wannan masifa haka kuma mu ke ba su kayan aiki fiye da a baya. Abu ne da ke bukatar cin makudan kudade sannan mu a nan Sahel muna fama da illolin canjin yanayi inda ake fuskantar fari akai-akai kamar yadda ake ciki a yanzu haka, ana cikin matsanancin halin karancin abinci yayin da kudaden sufurin jiragen ruwa suka yi hauhawar da ba a taba ganin irinta ba sanadiyyar annobar corona a can farko kafin abin ya kazance sakamakon halin rikicin da ake ciki a Turai.

Ya kara da cewa tsadar takin zamani ta kai matsayin da a yau lamarin na hana mu barci, babbar damuwarmu a yau ita ce ya zamu yi mu samar da wadatar takin zamani a daminar da ke tafe?

Babban sakataren ya tabbatar da cewa Majalisar Dinkin Duniya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen karfafa wa Nijer gwiwa a fadi tashin da take yi, inda dubun dubatar ‘yan gudun hijirar cikin gida da na kasashe makwabta suka tsere wa tashe tsahen hankula.

A gobe Talata Antonio Guterres zai isa gundumar Ouallam da ke iyakar Nijer da Mali don jin damuwar ‘yan gudun hijira da bukatun al’umomin da suka basu mafaka, a ci gaba da neman hanyoyin mayar da ‘yan gudun hijirar garuruwan da suka fito bayan lalacewar sha’anin tsaro a arewacin Mali.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG