A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin fafutuka sun shigar da kara a kotun birnin Yamai don ganin lauyan gwamnatin kasar ya fara sauraren karar manyan jami’an da kotun kula da yadda aka kashe kudaden kasa ta ce ta gano da rubda ciki akan dukiyoyin jama’a.
Tun a watan Afrilun da ya gabata ne kotun Cour des Comptes mai kula da yadda aka kashe kudaden kasa a rahoton binciken da ta fitar ta ayyana sunayen wasu ministoci da manyan darektocin gwamnati da masu zaman kansu da handame kudaden jama’a.
Sai dai har izuwa wannan lokaci ba a maganar gurfanar da wadanan mutane, dalili kenan da kungiyar Rotab da Tournons la Page suka garzaya kotu domin ankarar da lauyan gwamnati abin da al’ummar Nijar ke jira daga gare shi kamar yadda shugaban kungiyar yaki da cin hanci ta RNAC Adamou Oumarou ya bayyana.
A washegarin darewarsa kujerar mulki shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bukaci kungiyoyin fararen hula su ba shi goyon baya a yaki da cin hanci da mahandama dukiyar kasa sabili kenan wadanan kungiyoyi ke cewa sun yi nasu aiki a yanzu ya rage nasa .Malan Ali Idrissa shine shugaban kungiyar ROTAB.
A ci gaba da neman hanyoyin da za su taimaka haka ta cimma ruwa kungiyoyin sun bayyana shirin soma tuntubar al’ummar Nijar don samun hadin kanta a wannan yunkuri na yi wa kai da kai.
Misalai na barnar da aka tafka a wuraren da kotun ta cour des comptes ta gudanar da bincike na nunin wasu sun yi amfani da annobar covid 19 don yin cuwa-cuwa inda suka ce sun sayi kowace katifar kwanciyar mutun 1 akan 416000 f cfa hade da kowane kofin shan shayi akan 10000f cfa yayin da a wata kwangilar ta daban aka ce an yi odar buhun hatsi a 105,000 f cfa sai ban dakin da aka ayyana cewa an gina akan miliyan 40 f cfa wanda kuma a cewar masana darajar irinsa ba za ta wuce miliyan 2,5 fcfa.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: