Majalisar Dinkin Duniya ta nada tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issouhou a matsayin jagoran kwamitin da ke da alhakin nazarin hanyoyin magance matsalolin tsaro da na canjin yanayi a yankin Sahel.
Sai dai ‘yan kasar ta Nijar na bayyana ra’ayoyi mabambanta game da irin gudunmowar da tsohon shugaban kasar zai bayar wajen ganin an cimma burin da aka sa gaba.
Wani shirin hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afirka ne ya bukaci tsohon shugaban na Nijar Mahamadou Issouhou da ya jagoranci kwamitin kwararru domin zakulo hanyoyin da za su ba da damar shayo kan matsalolin da suke haddasa tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin sahel.
Kazalika kwamitin zai binciko shawarwarin da za su taimaka a tunkari illolin canjin yanayi da nufin samar da ci gaba a yankin da aka ayyana a matsayin mafi fama da wannan masifa a duniya.
Alhaji Assoumana Mahamadou daya daga cikin mashawartan Issouhou Mahamadou a zamanin da yake shugabancin kasa ya yaba da zabin tsohon shugaban.
Sai dai shugaban jam’iyar Moddel Ma’aikata, Tahirou Guimba, na ganin alamun an yi zaben tumun dare.
A ziyarar da ya kammala a Talata a Nijar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce sun cimma matsaya da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mamahamat akan batun damka ragamar kwamitin da zai binciko hanyoyin magance matsalolin da suka addabi yankin Sahel a hannun Mahamadou Issouhou.
A washegarin saukarsa daga karagar mulki tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issouhou ya kafa gidauniyar da aka kira Fondation Issouhou mahamadou FIM a takaice, wacce za ta maida hankali wajen nazari da bincike a fannin tsaro da neman hanyoyin magance illolin canjin yanayi.
Ko da yake, wasu ‘yan Nijar na ganinta a matsayin wata kungiya mai kokon bara.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga birnin Yamai: