Ofishin jakadancin Faransa a Jamhuriyar Nijar ya gudanar da aikin tantance sojojin da suka kafsa yakin “Indo China War” daga 1949 zuwa 1954 da nufin karrama su saboda yadda suka taya wannan yaki da ya barke a washegarin kammala yakin duniya na 2.
Sai dai kawo yanzu mutun daya tak ne aka gano a raye daga cikin wadannan barade.
Dakaru Afrikawa sama da 1000 ne kasar Faransa ta tura zuwa yakin na Indo China War wato guerre Indo Chine wanda aka shafe shekaru 5 ana gwabzawa a wani lokacin da ake kokarin murmurewa daga tashin hankalin yakin duniya na biyu.
Daya daga cikin sojojin da suka gwabza yakin na Indochine Alhaji Amadou Sami na tunawa da lokacin da hukumomin mulkin mallaka na Faransa suka tattara su zuwa Senegal akan hanyar tafiya fagen daga.
Sai dai gomman shekaru bayan wannan yaki ba wani abin a zo a gani da suka samu daga Faransa in ji tsohon soja Alhaji Amadou na garin Jouchi gundumar Tessaoua.
Ofishin jakadancin Faransa a Nijar ya kaddamar da ayyukan tantance irin wadanan sojoji don yi masu sakayyar goyon bayan da suka ba ta a zamanin wancan yaki kuma kawo yanzu wannan dattijo dan shekaru 100 a duniya Alhaji Amadou, shi ne kadai dayan sojan yakin Indo-chine dake raye dalili kenan aka bukaci ya zo birnin Yamai don gabatar da kansa.
Tsohon soja Alhaji Amadou Sami na da ‘yaya a kalla 52 cif. Abdoulaye Amadou da ake yi wa lakanin Dan Bayero ya koma gida kusa da mahaifinsa domin ba shi kulawar da ta dace.
Faransa wacce ke kan gaban kasashen da suka ci moriyar al’umomin Afrika a zamanin mulkin mallaka ta sha suka a shekarun baya sakamakon rashin biyan kudaden diyya ga Afrikawa ‘yan mazan jiyan da suka kafsa yaki a karkashin tutarta daidai da abin da take biyan takwarorinsu ‘yan asalin kasar, lamarin da ya sa gwamnatin Faransar ta shiga yunkurin daukan matakai don gyara wannan kuskure.