Sabanin yadda a shekarun baya ake shirya shagulgula da dama domin karrama ranar 3 ga watan Mayu, a wannan karon Cibiyar ‘Yan Jarida Maison de la Presse ta takaita abin ne da sanarwar bitar halin da aikin jarida ke ciki a Nijer, kasar da rahoton kungiyar kasa da kasa ta RSF na 2021 ya ayyana a matsayin ta 59 daga cikin kasashe 180 abin da ke nufin ba ta cira daga matsayinta na 2020 ba, duk kuwa da cewa a bayan nan hukumomi sun dauki matakin sassauci ga ‘yan jarida masu rubutu a yanar gizo gizo. Souleyman Oumarou Brah shine sakataren yada labarai a Cibiyar ta Maison de la Presse, ya na mai bayyana muhimacin ranar da kuma makomar aikin.
Shigowar kafafen sada zumunta a zamantakewar jama’a, a yau wani al’amari ne da ake ganinsa tamkar wata barazana ga makomar aikin jarida, to amma a cewar wani dan jarida mai zaman kansa, Souley Mage, ba kare bin damo.
Halin matsin tattalin arzikin da kafafe masu zaman kansu ke ciki wata matsala ce da ke iya shafar ‘yancin aikin jarida da na fadin albarkacin baki, alhali su ne ma’aunin mizanin dimokradiyya a kowace kasa. Cibiyar ‘yan jaridar na ankarar da gwamnatin Nijer akan wannan batu.
Yanayin da ‘yan jarida mata ke cikinsa a yayin gudanar da wannan aiki, ita ma wata matsala ce da ake ganin ta na maida hannun agogo baya, a kokarin tabbatar da cikakken ‘yancin aikin jarida da na fadin albarkacin baki . Balkissa Hamidou da Ousseina Harouna na cewa haka maganar take.
Saurari cikakken rahoton Suleiman Barma: