Da sanyin safiyar Larabar nan ne dai yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fara aiki, lamarin da ya kawo dakatar da yakin da shugabannin Amurka da na Faransa suka ce zai iya samar da wata hanyar da za a sake yin sulhu a zirin Gaza.
Birtaniya ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana a ranar litinin bayan da wata mahaukaciyar guguwa irinta ta biyu ta afkawa kasar a karshen mako, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla biyu tare da kawo cikas ga tafiye tafiye da jiragen kasa.
Hukumomin Najeriya na neman hanyar kaddamar da babban Shirin kare cin zarafin jinsi, ko GBV a fadin kasar.
Wani rahoto da wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa Equality Now ta fitar, ya ce ma’anar fyade a kasashen Afirka 25 ya ba da dama ga masu aikata laifuka su tafiyarsu ba tare da an tuhumesu wani laifi ba.
Gwamnatin kasar Chadi ta fada a ranar Talata cewa daruruwan mayakan Boko Haram na ficewa daga yankin tsakiyar Afirka suna tsallakawa zuwa kasashen Kamaru da Nijar da kuma Najeriya.
Mambobin kungiyar ‘yan tawaye tara dake neman a sako hambararren shugaban kasar Nijar sun mika wuya a jiya litinin, kamar yadda jami’an kasar da sojoji ke mulka suka bayyana.
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris na da wakilai 179 na zabe, yayin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya samu wakilai 214.
A yammacin ranar Talata ne sakamakon zabe ya fara fitowa fili a zaben shugaban kasa tsakanin mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da tsohon shugaban kasar Donald Trump.
Amurkawa sun kada kuri’unsu domin zaben wanda suke so su aika zuwa fadar White House na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Haka kuma za su zabi wadanda za su cike kujerun Majalisar Dattawa 34, sai kuma ‘yan Majaisar Wakilai 435 da kuma gwamnonin jihohi 13.
Dubban masu zanga-zanga ne suka taru a duk fadin kasar Isra'ila don nuna adawa da korar ministan tsaro Yoav Gallant, da firaminista Benjamin Netanyahu ya yi a ranar Talata.
Hukumomin Najeriya na shirin sauya motoci miliyan 1 masu amfani da injinan man fetur zuwa amfani da iskar gas mai rahusa, ko CNG, nan da shekara ta 2027.
Dubban jama'a ne suka taru a ranar litinin a kan titunan birnin Yaounde, suna ta raha don yin maraba da shugaban Kamaru da ya dade ba ya kasar.
Shirin Ciki Da Gaskiya na wannan mako kashi na biyu a tattaunawar da muke kan takaddamar da ta kunno kai a garin Garba Chede na Jihar Taraban Najeriya, inda ake zargin wani Sarki da kwace filayen jama'a, zargin da Sarkin ya musanta
Shirin Ciki Da Gaskiya na wannan mako ya yi nazari ne kan takaddamar da ta kunno kai a garin Garba Chede na Jihar Taraban Najeriya, inda ake zargin wani Sarki da kwace filayen jama'a, zargin da Sarkin ya musanta.
Masu ruwa da tsaki a fagen noma na kungiyar (AgTech) na taro a kasar Kenya, domin lalubo hanyar da za a bunkasa karfin noma wajen ciyar da al'ummar Afirka.
Cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya CDC, ta ce cutar kwalara da mace-mace sun karu da fiye da kashi 200 a bana idan aka kwatanta da na bara.
Domin Kari