Ya zama mai muhimmanci ‘yan Najeriya su kawar da bambance-bambancen kabilanci, wariya don addini da yanki matukar kasar za ta tsira daga talauci, rashin tsaro da guguwar ‘yan a fasa kowa ma ya rasa.
Alkalin kotun Isma'ila Abdullahi ya tura Jaruma gidan yari don jiran beli a ranar Juma’ar nan mai zuwa.
Wata sabuwar kungiyar masu matsakaicin shekaru a dattawan arewa sun karfafa cewa zabar dattawa masu karancin shekaru a 2023 ne zai kawo maslahar tsaro da tattalin arziki.
Babban daraktan ofishin gwamnonin APC Salihu Lukman wanda ya mika takardar murabus din sa, ya ja hankalin jam’iyyar da cewa babban taron ta na zabar sabbin shugabanni shi ne zakaran gwajin dafin tabuka abun kirki a zaben 2023.
Daya daga mazauna kauyukan karamar hukumar Anka a jihar Zamfara, Murtala Waramu ya ce shi da sauran jama’a sun kirga gawa 52 da ‘yan bindiga su ka yi wa kisan gilla a wani mummunan farmaki da su ka kai.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna nasarorin da kasar ta samu duk da kalubalen tsaro da koma bayan da annobar coronavirus ta haifar wa kasar.
Duk da tsarin dimokradiyya da a ke yi a Najeriya, masu sharhin sun ce ba a samun bambancin manufofin ‘yan siyasa a kowace jam’iyya ba, don tsarin jari hujja da ke nisanta talakawa da masu hannu da shuni ya kulla dangantaka tsakanin su.
Yayin da a ke haramar shiga sabuwar shekara ta 2022, ‘yan Najeriya na nuna matukar damuwa kan shirin gwamnati na janye dukkan tallafin man fetur da hakan zai sa lita ta kai Naira 320-340 daga Naira 162.
Wani kalubale da masana ke hange shi ne irin dambarwar da za a samu a tsakanin manyan jam’iyyu na tsaida ‘yan takarar shugaban kasa tsakanin kudu da arewa.
Majalisar limaman Islama ta yankin Sahel a Afirka wato Rabidatul Islam Fi Biladi Sahel ta kammala taro kan lamuran tsaro a Abuja, babban birnin Najeriya da ganawa ta musamman da kungiyar JIBWIS.
A baya, babban bankin Najeriya ya daina ba da dala ga kasuwar canji inda ya bukaci duk mai son dala ya nufi bankin sa don samun ta kan farashin hukuma.
Wasu ‘yan siyasa daga Arewaci da Kudancin Najeriya sun kafa gwamnati ko kungiyar sa ido kan ayyukan gwamnati mai ci da su ke zayyanawa da cewa ta gaza.
Cibiyar ba da lasisin kwarewa kan ayyukan kwangiloli ta Najeriya “Chartered institute” ta ce za ta fara daukar matakan gurfanar da wadanda ba su da lasisi a jami’an da kan gudanar da ayyukan kwangiloli don yaki da baragurbi.
Masana tattalin arziki a Najeriya da ma jami’an gwamnati na duba yanda rabon arzikin kasa zai iya amfani har mutane su shaida sun gani a kasa.
Akalla wakilai 3,600 suke halartar babban taron, wanda za a gudanar a ranakun Asabar da Lahadi a Abuja.
Yayin da gwamnati ke cewa dakarun tsaro na birkita lissafin miyagun iri, jama’a na cewa miyagun na sauya dabarar hallaka jama’a ne da mallake dukiyarsu.
A jumma'ar nan Najeriya ke cika shekaru 61 da samun 'yanci daga Burtaniya daga lissafin karbar 'yancin a ranar daya ga watan Oktoba na 1960.
Dalar Amurka na cigaba da tashin gauron zabi a Najeriya duk da barazanar cafke shugaban dandalin bayanan farashin canji na Aboki FX da gwamnan babban bankin Najeriya ya yi.
Babban Shehun darikar Tijjaniyya a Najeriya Dahiru Usman Bauchi ya ce ba su yarda wasu su dau doka a hannu ta hanyar ramuwar gayya bisa kisan gilla ga mabiyansa ba a Jos, wadanda suke komawa jihohinsu bayan ziyarar da su ka kai masa a Bauchi.
Shugaban na magana ne bayan samun rahoton da ke nuna kashi 2.5% na fadin kasar Najeriya a ke amfana da ita wajen aikin noma.
Domin Kari