Matasan dattawan sun ba da misali da shugabannin Najeriya na soja da farar hula da su ka yi ayyukan kirki don lokacin da su ka hau karaga su na da kwarin jiki da lafiya.
A zantawar sa da Muryar Amurka a Abuja, shugaban kungiyar Alhaji Umar Gital ya ce don samun abun da a ke bukata na aiki tukuru ya sa gwamnati ta tsara mutum ya yi ritaya in ya cika shekaru 60 na haihuwa ko 35 na aiki.
Gital ya ce da shugaba da wanda zai yi mataimaki duk ya dace a hada masu sabon jini a jiki kuma a duba cancanta ba tare da lalle sai an dage wajen duba arewa ba ne ko kudu.
Da ya ke magana kan lamuran tsaron shugaban amintattu na gamayyar matasan Arewa Nastura Ashir Sharif ya ce ko waye ya samu shugabanci sai ya dau dabarun a ciza a hura kafin samun nasara.
A na sa bangare mukarrabin shugaba Buhari, Faruk Adamu Aliyu ya ba da baki ne ga ‘yan bindiga da su duba kadun ‘yan uwan su talakawa da kan zama mafi yawan masu shan wahala da kuma matsalolin ke shafa.
Duk da cewa a ranar 23 ga Fabrairun badi ne a ke sa ran gudanar da babban zabe a Najeriya, tuni masu sha’awar takara daga manyan jam’iyyu ke bayyana manufa.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya cikin sauti :