Shehu Dahiru Bauchi wanda ke magana a taron manema labarai a Abuja, ya bukaci gwamnati da ta ba da diyyar rayukan da aka rasa.
Malamin ya ce duk hakkin kare rayukan jama'a na wuyan gwamnati don haka ta tabbatar da hukunta masu hannu a tare masu zikirin don hakan ya zama darasi ga masu niyyar aikata irin haka a nan gaba.
Shehu Dahiru Bauchi wanda ya yi ta'aziyya ga iyalan almajiran na sa da su ka rasa rai, ya ba da kwarin gwiwar irin akasin ba zai sake faruwa ba.
Da ya ke ta'aziyya ga iyalan mamatan,Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya jinjinawa iyaye da masu fada a ji don kwantar da sabuwar fitina, ya na mai nuna gamsuwa ga matakan da gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ke dauka.
Shi ma mawallafi a Jos Alhaji Ibrahim Ibzar ya ce matukar za a rika hukunta masu muguwar dabi'a za a yi rigakafin mugun aiki.
Ba mamaki yanayin jihar Filato na ramuwar gayya, ya sanya hukumomi a jihar kafa dokar hana fita dare da rana a yankin Jos ta arewa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya: