Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Kirga Gawarwaki 52 Da ‘Yan Bindiga Su Ka Kashe A Kauyukan Anka - Murtala Waramu


Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.
Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.

Daya daga mazauna kauyukan karamar hukumar Anka a jihar Zamfara, Murtala Waramu ya ce shi da sauran jama’a sun kirga gawa 52 da ‘yan bindiga su ka yi wa kisan gilla a wani mummunan farmaki da su ka kai.

Murtala wanda yake cikin masu gudun hijira a Anka a jihar Zamfara ya ce har yanzu sun a ta binciken sauran mutane da ba a gani ba don sanin ko su na raye ko kuwa a’a.

Murtala ya ce da sun samu kwarin guiwa daga jami’an tsaro, za su iya fatattakar barayin da amfani da bindigar su ta harbi-ka-ruga.

A yanzu dai a cewar Murtala, mutane sun samu an bude mu su makarantun firamare a garin Anka a jihar Zamfara inda su ke samun mafaka.

Da alamun kurar harin ta lafa don ‘yan bindigar sun wuce da kungurmin daji bayan sace dabbobin gida da jama’ar kauyukan ke kiwo.

XS
SM
MD
LG